Syria: Yara miliyan 5 na cikin wani hali

Yaran Syria Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yara da mata na cikin miliyoyin 'yan gudun hijiran Syria

Wani sabon rahoto da Asusun tallafawa yara na majalisar dinkin duniya, UNICEF ya fitar ya nuna cewa yawan yaran da yakin da ake a Syria ya shafa sun kai 5.5 miliyan.

Asusun ya kuma ce kimanin yara miliyan daya daga cikinsu na cikin wani hali na karancin abinci da magunguna a guraren da aka yiwa kawanya.

UNICEF ya nemi a kawo karshen tashin hanklin da ake yi a Syria nan take, inda ya nemi a kuma bada damar kai kayan agaji ga yaran da yakin ya rutsa da su.

An shiga shekara ta uku kenan da fara yaki a kasar ta Syria.