Shugaban Ukraine ya nemi agajin sojin sa-kai

Hakkin mallakar hoto
Image caption Mr Turchynov ya bukaci samar da dakarun sa-kan ne yayin da zaman dar-dar ke karuwa da Rasha kan Crimea

Shugaban rikon kwarya na Ukraine, Oleksandr Turchynov, ya nemi da a kirkiro wata rundunar tsaron kasa ta sojin sa-kai da za ta taimaka wajen kare kasar.

Ya ce za a sirka wasu daga cikin dakarun sojin sakan ne da suke da kwarewa ta aikin soji aiki da sojojin kasar.

Mr Turchynov, ya kuma sheda wa kamfanin dillancin labarai na Faransa, AFP, cewa manyan jami'an gwamnatin Rasha sun ki yarda da duk wata ganawa da takwarorinsu na Ukraine.

A ranar Lahadi ne al'ummar Crimea, za su kada kuri'ar raba gardama, ta neman komawa karkashin Rasha, kuma tuni daman dubban dakarun Rasha sun kama iko da yankin.