An sace mana shanu 500 a Jos - Fulani

Garken shanu Hakkin mallakar hoto Harry Hook
Image caption Rikicin Fulani da manoma ma wata babbar matsala ce a yankin

Fulani makiyaya a jihar Pilato dake tsakiyar Nigeria na kukan cewa an sace musu shanu fiye da 500, a karamar hukumar jos ta kudu.

Sun ce suna da masaniyar inda aka kai shanun a kauyen Vom, amma jami'an tsaro ba sa son basu kariya, domin zuwa can su karbo shanunsu.

Fulanin na zargin 'yan kabilar Berom da sace musu shanun a karshen makon jiya.

A mafi yawancin lokuta batun satar shanu na janyo rikicin kabilanci da na addini a tsakiyar Najeriya.