Crimea: Kungiyar G7 ta gargadi Rasha

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaban Rasha, Vladmir Putin

Kungiyar kasashe bakwai masu karfin tattalin arziki ta yi kira Rasha ta dakatar da dukkan wani yunkuri na mayar da yankin Crimea na Ukraine karkashin ikonta ko kuma adauki mataki akanta.

A cikin wata sanarwa kungiyar ta G7 ta ce kuri'ar raba gardama wanda Rasha ke marawa baya da za'a gudanar a ranar Lahadi mai zuwa ba zai sami wani halacci a bisa doka ba kuma ba za'a amince da ita ba.

Shugabannin na G7 sun ce za su dauki mataki a daidai kunsu da kuma a kungiyance idan Rasha ta nemi shigar da Crimea cikin kasarta.

Shugaban Amirka Barack Obama ya ce "abin da ba zai yiwu ba shi ne Rasha ta yi gaba gadi ta zuba sojojinta tare da karya dokokin kasa da kasa".

Karin bayani