Ban yi murabus ba - Gusau

Hakkin mallakar hoto gusau facebook
Image caption Janar Aliyu Muhammed Gusau

Sabon Ministan tsaron Nigeria, Janar Aliyu Muhammed Gusau ya shaidawa BBC cewar bai sauka daga kan mukaminsa ba.

Janar Gusau ya bayyanawa BBC ta wayar tarho cewar ba gaskiya bane rahotannin dake cewar ya sauka daga kujerarsa ta ministan tsaron Nigeria.

Tun farko, wasu rahotanni sun ce ministan tsaron ya gabatar da wasikar yin murabus a sakamakon wani sabani da aka samu tsakaninsa da manya-manyan hafsoshin sojan Nigeria.

A taron mako-mako na majalissar ministocin kasar, Ministan yada labarai na Nigeria, Mr Labaran Maku, ya tabbatarwa 'yan jarida cewar Janar Aliyu Gusau bai halarci taron ba.

A makon da ya gabata ne Shugaba Goodluck Jonathan ya nada Janar Aliyu Muhammed Gusau a matsayin ministan tsaron kasar.

Karin bayani