Jonathan ya sa a binciki batan Dala biliyan ashirin

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Gwamnatin Jonathan na shan suka saboda wannan zargin

Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan ya bada umurnin a gudanar da binciken kwakwaf a kan asusun kamfanin man fetur na kasar watau NNPC.

A ranar Laraba fadar shugaban kasar ta bada sanarwar umurnin, makwanni bayan da aka zargi kamfanin da kin bada bayanai kan kusan dala biliyan 20 na harajin man fetur.

Gwamnan babban bankin kasar, Sanusi Lamido Sanusi a watan da ya gabata ne ya bayyanawa kwamitin bincike na majalisar dattijan Nigeria cewar kamfanin NNPC bai saka kudin danyen mai kusan dala biliyan 20 ba.

Kamfanin NNPC ya musanta wannan zargin.

Kwanaki kadan bayan Malam Sanusi ya fasa kwoi sai shugaba Jonathan ya dakatar da shi daga mukaminsa.

Sanarwar fadar shugaban kasar ta ce wannan babban kamfanin kasa da kasa ne za ta gudanar da binciken.

Karin bayani