Jirgin ruwa ya kife a Lagos ta Nigeria

Tawirar Najeriya
Image caption Tawirar Najeriya

Hukumar kai agajin gaggawa ta Najeriya NEMA, ta ce ana ci gaba da aikin ceto, domin gano gawawwakin mutanen da ruwa ya ci, bayan wani jirgin ruwa ya kife a jihar Lagos.

Kawo yanzu an gano gawawwakin mutane 20, tun bayan aukuwar al'amarin a ranar Talata da daddare, a karamar hukumar Festac Town.

Ba wannan ne karo na farko ba da ake samun kifewar jirgin ruwa a yankin, abin da ya sa karamar hukumar ta raba wa mutanen yankin rigar kariya daga nutsewa a ruwa.

Festac na wutsiyar ruwan tekun Atlantika, kuma al'ummar karamar hukumar na gudanar da harkokinsu ne a kan ruwa.