Jirgin Malaysia: an ga wasu hotuna

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan uwan wasu daga cikin fasinjojin cikin jirgin ne ke kuka

China ta wallafa hotunan tauraron dan-adam na wasu manyan abubuwa da ke yawo akan tekun kudancinta, da ka iya zama tarkacen jirgin Malaysian nan da ya bata ranar Asabar.

Tauraron ya dauki hotunan ne kwana daya bayan da jirgin ya bace akan hanyarsa ta zuwa Beijin, kuma mafi girma daga cikin abubuwan ya kai fadin mita 24.

Kasashen Malaysia da Vietnam, sun ce sun tura jiragen sama wurin domin su duba abubuwan.

Sai dai kuma shugaban hukumar sufurin jiragen saman fasinja na China, ya ce, babu tabbas cewa abubuwan da aka gano a hoton na jirgin Malaysian ne.