Har yanzu babu duriyar jirgin Malaysia

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu bincike a cikin teku

Gungu-gungu na jama'a suna can suna ta bincike a sassan teku da ke gabas da yammacin Zirin Malay, bayan da akai ta samun rahotannin da ke saba wa juna game da makomar jirgin saman nan da ya bace ko kasa ko sama kwanaki biyar baya, a kan hanyarsa zuwa Beijing daga birnin Kuala Lumpur.

A wani taron manema labarai, Malaysia ta bayyana cewa na'urar hangen nesa ta soji ta hango wani abu da ba a tabbatar da ko mine ne ba a tsibirin Malacca - wanda zai iya kasancewa jirgin saman da ya bacen ne.

Wasu jiragen ruwan Amurka guda biyu suna taimakawa wajen binciken.

Mai magana da yawun rundunar sojin ruwan Amurka Kwamanda William Mark ya ce an fara fidda tsammanin samun wani wanda ya tsira da ransa.

Karin bayani