Za a yanke wa Hoeness hukunci

Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Hoeness wani fitaccen dan kwallo ne da aka taba yi a Jamus

A ranar Alhamis ake sa ran kammala shari'ar shugaban kulob din Bayern Munich, Uli Hoeness wanda ya amince da laifin kin biyan haraji.

Hoeness ya ce yakamata ace ya biya gwamnatin Jamus kudin euro miliyan 27, sakamakon hada-hadar da ya yi a kasuwar shunku ta hanyar wasu asusun bankin Swiss.

Ana sa ran za a yanke masa hukuncin zaman gidan kaso.

Uli ya yi niyyar yin murabus daga matsayinsa na Bayern Munich, amma yadda magoya bayan kulob din suka rinka kiran sunansa, yasa dole ya janye.