"Yanayin mutum kan bazu a Facebook"

Mahajojin dandalin sada zumunta Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Mutane na amfani da manhajojin dandalin sada zumunta a salula da kwamfutocin tafi da gidanka

Wani bincike na jami'ar California, Yale a Amurka ya nuna cewa, yanayin da mutane ke ciki na iya yaduwa a dandalin sa da zumunta, kamar Facebook.

Binciken ya yi amfani da tsokacin miliyoyin masu amfani da shafin Facebook, inda ya duba tasirin ruwan sama.

Masu binciken sun gano cewa ta hanyar mutum guda da ruwan sama ya shafa, hakan na tasiri a kan wasu karin mutane biyu.

"Magana a kan yanayin da mutane ke ciki a wani guri, kan bazu a duniya a rana guda,"

Sun duba tsokacin mutane abokan wandanda ruwan sama ya shafa, da kuma wadanda ke zaune a biranen da yanayinsu ke da dan dama-dama.

Sakamakon ya nuna cewa duk tsokaci na bakin ciki guda daya, kan janyo wasu irinsa 1.29 fiye da yadda aka saba gani, a tsakanin abokai.

Haka kuma abin mamakin shi ne, tsokaci na farin ciki ya fi tasiri sosai, inda yake janyo irinsa 1.79.

A cewar masu binciken "Hakan na nufin cewa yanayi ko halin da mutane ke ciki, kan yadu ta dandalin sa da zumunta, ta yadda ya kan kai ga samun tarin mutanen dake samun kansu cikin farin ciki ko kuma bakin ciki."

"A sakamakon haka za mu iya ganin karuwa game da yanayin da mutane ke ciki a duniya, da zai iya janyo karin rashin tabbas game da komai, kama daga siyasa zuwa tattalin arziki. "