Merkel ta gargadi Putin kan Ukraine

Hakkin mallakar hoto RIA Novosti
Image caption Shugaba Merkel da Shugaba Putin

Shugabar Gwamnatin Jamus, Angela Merkel ta gargadi Rasha cewar idan ta ci gaba da dagula al'amura a makwabciyarta Ukraine, abin zai zama babban bala'i.

A cewarta, matsalar ba Ukraine da kungiyar Tarayyar Turai- EU kadai za ta shafa ba, amma har da ita kanta Rashar.

A jawabinta ga majalisar dokokin Jamus a Berlin, Mrs Merkel ta ce idan Rasha ta ki canza matsayinta, shugabannin kungiyar EU sun shirya daukar matakin da zai shafi tattalin arziki.

A ranar Laraba, Shugaba Obama ya bukaci Rasha ta kawo karshe kaka-gidan da ta yi a yankin Crimea ko kuma a kakaba mata takunkumi.

Obama ya gana da Firaministan riko na Ukraine, Arseniy Yatsenyuk a fadarsa ta White House inda ya ce kasa daya ba za ta yi wa sauran barazana ba.

Karin bayani