Israila ta kai wa Gaza hari

Janaizar wani dan Falasdinu Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Janaizar wani dan Falasdinu

Sojin Israila sun kai wa zirin Gaza hari ta sama bayan da mayakan Falasdinu suka harba rokoki a kudancin Israila.

Kakakin gwamnatin Israila ya ce wurare 29 ne aka kaiwa hari sai dai ba a bayana ko an samu asarar rayuka ba.

Da farko dai mayakan kungiyar da ake kira Islamic jihad sun rika harba rokoki zuwa yankin kudancin Israilar .

Kungiyar ta ce tana son ta rama mutuwar wasu mambobinta su uku da aka kashe a harin da Israilar ta kai ta sama ranar talatar da ta gabata.