An sako kawun Shugaba Jonathan

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan sanda na kokarin tabbatar da tsaro a jihar Bayelsa

'Yan sanda a jihar Bayelsa dake yankin Niger-Delta a Nigeria sun ce an kubutar da kawun Shugaba Goodluck Jonathan, Cif Nengite Nitabai wanda aka sace kusan makwanni uku da suka wuce.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Mr Hilary Okara wanda ya tabbatar da hakan, ya ce an kubutar da Cif Nitabai mai shekaru 70 a duniya a yankin Odioma na karamar hukumar Brass ta jihar.

A cewarsa, kawun shugaban kasar na cikin koshin lafiya kuma tuni ya hade da sauran iyalansa.

Mr Okara ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Nigeria-NAN cewar an damke mutane shida da ake zargin suna da hannu a sace dattijon.

Rahotannin da ake samu lokacin da aka sace Cif Nitabai sun ce iyalansa sun yi tayin bada naira miliyan 30 don a sako shi amma masu garkuwa da shi sun bukaci a basu naira miliyan 500.

Karin bayani