Kano: Sabon salo na satar jama'a

Wasu 'yan sandan Najeriya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu 'yan sandan Najeriya

Hukumar tsaron farin kaya wato SSS a jihar Kano dake Arewacin Najeriya ta gargadi jama'ar jihar kan wani sabon salo da ta ce yanzu wasu na amfani da shi wajen sace mutane domin neman fansa.

Hukumar ta SSS ta ce a yanzu dabi'ar barazana da sace mutane domin neman fansa na karuwa a jihar ta Kano, abin da ya sa kenan ta ke kira ga jama'a da su kara hattara.

Haka kuma hukumar ta ce ta samu nasarar kame wasu mutane da ake zargi da sace wani yaro dan shekara 7 da kuma kashe shi bayan an ba su kudin fansa.

A 'yan watannin nan dai, matsalar sace mutane domin neman kudin fansa ta bulla a Arewaci Najeriya, amma ba wani sabon abu ba ne a kudancin kasar inda matsalar ta zama ruwan dare.

Karin bayani