'China ta yi kuskure a kan hotunan jirgi'

Hakkin mallakar hoto v
Image caption Kwanaki shida kenan ana neman jirgin saman

Hukumomi a Malaysia sun ce akwai kuskure a hotunan tauraron dan-adam da China ta wallafa a matsayin baraguzan jirgin saman Malaysia wanda ya bace tun ranar Asabar.

Ministan sufurin Malaysia, Hishammuddin Hussein ya shaidawa manema labarai a Kuala Lumpur cewar hukumomin China sun tafka kura-kurai a kan wadannan hotunan.

Ya karyata rahotannin da ke cewar an samu bayanai game da inda jirgin ya dosa bayan ya bace ko sama ko kasa.

Jirgin mai dauke da mutane 239 na kan hanyarsa ta zuwa China ne daga Malaysia kuma daga cikin fasinjojin hadda 'yan China 150.

Karin bayani