Ana cigaba da farmaki a kan al Shabaab

Ta'adi bayan artabu a Somalia Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ta'adi bayan artabu a Somalia

Rahotanni sun ce, dakarun Tarayyar Afruka da na gwamnatin Somalia sun kwace wani gari mai mahimmanci ta fuskar tsaro, a arewacin birnin Mogadishu.

Sun samu nasarar ce a cigaba da babban farmakin da suke kaiwa a kan mayakan Islama na Al Shabaab.

A cewar jami'ai, a yanzu 'yan Al-Shabaab sun janye daga garin Buloburde, inda daga nan ne ake zuwa sauran sassan tsakiyar Somaliyar.

Majalisar dinkin duniya na goyon bayan farmakin sojan, amma kuma ta yi gargadin cewa, fadan zai iya yin mummunan tasiri a kan fararen hula kimanin miliyan uku.

An ce mutane dayawa na ta tserewa daga yankin.

Karin bayani