An kashe masu zanga -zanga biyu a Turkiya

Janai'zar matashin da aka kashe a Turkiya Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Janai'zar matashin da aka kashe a Turkiya

Rahotanni daga Turkiyya sun ce cewa mutane biyu sun mutu, yayin wata zanga zangar gama-gari a fadin kasar da ta biyo bayan jana'izar wani matashin yaro da tun a baya zangar zangar da ake yi ta adawa da gwamnati ta rutsa da shi.

Kafafen yada labarai na Turkiyyan sun ce dan zanga zanga daya ya mutu sakamakon raunin da aka ji masa a ka, yayin dauki ba dadi da 'yan sanda a birnin Santanbul.

Can a gabashin kasar kuma, rahotanni sun ce wani dansanda ya rasu sakamakon ciwon zuciya, yayin zanga zangar.

Mutuwar matashin yaron, Berkin Elvan, ranar Talata, wanda yake cikin halin rai kwakwai mutu kwakwai tun lokacin da aka harbe shi da gwangwanin hayaki me sa hawaye a Santanbul a watan Yuni ita ta kara rura wutar zanga zangar.