Ahmad Tejan Kabbah na Saliyo ya rasu

Image caption Ana tuna Mr Kabbah a matsayin wanda ya jagoranci kasarsa zuwa ga zaman lafiya

Tsohon shugaban kasar Saliyo, Ahmad Tejan Kabbah, ya rasu ya na da shekaru tamanin da biyu.

Ana dai tuna Mr Kabbah ne a matsayin wanda ya jagoranci kasarsa zuwa ga zaman lafiya bayan yakin basasa ya haddasa rasuwar fiye da mutane dubu dari da ashirin tare da sare gabban dubunnai da dama.

A shekarar 2002 ne rikicin ya kawo karshe bayan da dakarun kasashen waje suka taimaka aka murkushe 'yan tawayen kasar.

Mr Solomon Barewa minista ne a lokacin mulkinsa kuma ya bayyana shi a matsayin mutum mai matukar kishin kasa.