Arbeloa na murmure wa daga jinya

Alvaro Arbeloa Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Alvaro Arbeloa ya yi wasa a Liverpool da Bernabeu

Dan wasan baya na Spaniya, Alvaro Arbeloa na kokarin murmure wa, domin shiga gasar cin kofin duniya, ya na jinya na mako shida zuwa bakwai saboda raunin da ya samu a kaurinsa.

Dan kulob din Real Madrid din mai shekaru 31, na yawan buga wasa a rukunin farko na gasar cin kofin duniya da kuma gasar Zakarun Turai.

Ya samu raunin ne a karawarsu da Atletico Madrid a ranar 2 ga watan Maris.

"Raunin ya fi yadda ake tsammani, amma idan komai ya tafi dai-dai zan iya koma wa fili nan da makonni shida zuwa takwas." In ji Arbeloa.