An kubutar da dan majalisar Bauchi da aka sace

'Yan sandan Najeriya
Image caption A ranar Alhamis da daddare ne aka ceto dan majalisan

Rahotanni daga jihar Bauchi a arewacin Nijeriya na cewa, 'yan-banga da jami’an tsaro sun kubutar da 'dan-majalisar dokokin jihar da wasu 'yan-bindiga suka sace.

Kimanin kwanaki goma da suka gabata ne aka sace Yusuf Nuhu, a karamar hukumar Toro ta jihar.

Sai dai wata karamar yarinya ta rasa ranta a lokacin musayar wuta tsakanin bagarorin biyu, bayan harsashi ya karkace ya same ta.

A cewar 'yan sandan dan majalisar na cikin koshin lafiya, yayin da 'yan bindigar kuma suka arce bayan sun samu raunuka a musayar wutar.