CAR: Yunwa na halaka 'Yan gudun hijira

Hakkin mallakar hoto c
Image caption Kimanin 'yan Najeriya 400 ne ke zaune a kauyen Kenju dake Kamaru

'Yan gudun hijira daga rikicin Jamhuriyar tsakiyar Afrika da dama ne suka hallaka sakamakon matsananciyar yunwa sannan wasu da dama sun shiga cikin mawuyacin hali, yayin da suke kokarin tserewa daga kasar zuwa yankunan kasar Kamaru.

A kalla mutane sama da 50 ne suka hallaka cikinsu kuwa har da kananan yara 33 wadanda yunwa ta hallaka.

A yanzu haka dai kimanin 'yan Nigeria 400 ne ke zaune a kauyen Kenju dake jahar Bertuwa a kasar Kamaru, wadanda suka bayyana irin mawuyacin halin da suka tsinci kansu ciki, yayin da suke gudun hijirar.

Wannan rikici dai ya raba dubban mutane da muhallansu.