An yi garkuwa da Misrawa 70 a Libya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mayakan sa kai nada matukar karfi a kasar Libya

Wani jami'i a ma'aikatar harkokin wajen Masar ya ce, wasu 'yan bindiga a Libiya sun yi garkuwa da wasu Misrawa saba'in.

A cewar jami'in, 'yan-bindigar sanye da kayan soja, sun yi awon gaba da mutanen ne daga gidajensu da ke Tripoli, babban birnin Libiyar, kuma ba a da tabbacin ko 'yan-bindigar su wanene.

Jami'in ya ce, ministan harkokin wajen Masar na tuntubar takwaran aikinsa na Libiya don ganin an sako mutanen.

Ko a watan Janairun da ya wuce sai da aka sace Misrawa shidda a Tripoli, ciki har da jami'an diplomasiyya, kafin a sako su bayan 'yan kwanaki.

A Libiyar dai akwai mayakan sa kai masu ikon gaske, wadanda ba sa biyaya ga gwamnatin kasar.

Karin bayani