Jonathan ya umarci sojoji kai farmaki dajin Rugu

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Har yanzu mutane na ci gaba da zaman dar dar a yankunan da hare haren ya shafa

Rahotanni daga Nigeria na cewa Shugaba Goodluck Jonathan ya umarci rundunar sojin Kasar data kaddamar da farmaki kan dajin Rugu domin murkushe masu tayarda kayar baya wadanda ke kai hare hare a arewacin Kasar.

Haka kuma rahotannin sun ambato Shugaba Goodluck yana baiwa hukumar kai daukin gaggawa ta NEMA umarnin kai kayayyakin tallafi ga al'ummomin da hare haren baya bayan nan a jahar Katsina ya shafa.

Shugaban yana maida martani ne game da kashe kashen da wasu 'yan bindiga suka yi a kan al'ummomin Sabuwa da Faskari a Katsina inda suka hallaka mutane da dama tare da kona gidaje.

Tun farko dai wani dan majalisar dattijai daga Katsina ya yi zargin cewa hukumomin jahar sun maida hankali wajen ziyarar Shugaban Kasar Katsina ba tare da baiwa al'ummomin da hare haren ya shafa kariya ba.

Masu lura da al'amuran tsaro dai na ganin cewa matsalar tsaro na kara tagayyara a Najeriyar.