'Yar Pakistan ta mutu bayan ta kona kanta

Wani dan sanda a Pakistan Hakkin mallakar hoto Other
Image caption Yarinyar ta ce an yi mata fyaden ne a lokacin da take hanyar zuwa makaranta a watan Janairu

Wata yarinya 'yar Pakistan ta mutu, kwana daya bayan ta cinna wa kanta wuta.

To kona kanta ne domin nuna adawa da belin da aka yi wa wasu maza biyar da ta yi zargin sun yi mata fyade.

Jami'ai a kasar sun ce yarinyar mai suna Amina Bibi, mai shekaru 18 ta kona kanta a kofar wani caji ofis dake birnin Multan, ranar Alhamis.

Ta zargi 'yan sanda da kin yin bincike sosai game da karar da ta shigar kan wadanda tace sun yi mata fyade.