CAR: 'Yan Nigeria dake garin Kindu na cikin kunci

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan Nigeria dake garin Kindu na cikin mawuyacin hali

Wasu 'yan Najeriya mazauna Jumhuriyar Tsakiyar Afirka da suka gujewa rikicin da ake fama da shi a kasar, sun ce suna cikin wani mawuyacin hali a sansanin da suka samu mafaka a garin Kindu na kan iyaka da kasar Kamaru.

'Yan gudun hijirar wadanda yawansu ya kai dari hudu, sun ce sun shafe kusan watanni biyu a sansanin, amma babu wani taimako da suka samu.

Sun kuma yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta taimaka masu wajen mayar da su gida.

Rikicin Jumhuriyar Tsakiyar Afirkaya raba dubban mutane da gidajen su.