Ana zaman zullumi a kudancin Kaduna

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

A Najeriya, ana zaman zullumi a karamar hukumar Kaura dake jihar kaduna bayan wani tashin hankalin da yayi sanadiyar mutuwar mutane sama da dari.

Dazu ne aka kammala jana'izar mamatan.

Wani magabajin karamar hukumar ya shaidawa BBC cewa akwai mutane akalla dubu ukku da suke neman mafaka a wata makaranta dake bukatar magani da abinci.

Wasu mahara da ake zaton fulani ne, makiyaya, suka kai harin akan wasu kauyuka a kudan cin jihar ta Kaduna.

Karin bayani