An yi gangami a Rasha

Masu gangani a Rasha Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu gangami a Rasha

Dubban mutane sun yi gangami a tsakiyar Moscow, babban birnin Rasha domin nuna rashin amincewa da tura sojojin kasar zuwa yankin Crimea.

Wani dake halartar gangamin ya fadawa BBC cewa, yana ganin Rasha tana koma tamkar halin da ta samu kanta a lokacin mulkin Joseph Stalin.

Sai dai kuma wasu gungun mutanen daban sun halarci wani gangami na nuna goyon bayan gwamnatin Rasha, inda suka rika cewa, 'Crimea yankin Rasha.'

Karin bayani