Ukraine ta ce Rasha ta kai sojoji Crimea

Masu zanga-zangar adawa da kuma goyon bayan mamaye Crimea a Moscow Hakkin mallakar hoto AP AFP
Image caption Masu zanga-zangar adawa da kuma goyon bayan mamaye Crimea a Moscow

Ukraine ta zargi Rasha da yin amfani da karfin soja wajen mamaye yankinta dake arewacin Crimea.

Dakarun tsaron iyakokin Ukraine sun ce, jirage masu saukar ungulu da kuma motocin yaki masu sulke sun jibge soja fiye dari a wajen kauyen Strilkove:

Tuni dai hukumomin Ukraine suka bakaci Rasha ta janye nan take, kuma tace tana da hakkin yin amfani da kowacce hanya wajen dakile kokarin yi mata mamaya:

Karin bayani