An rufe filin jirgin saman Blantyre

Zirgin saman Malawi
Image caption Zirgin saman Malawi

Daruruwan fasjina ne suka samu kansu cikin halin tsaka mai bayan hukumomi a Malawi sun bada sanarwar rufe filin jiragen sama na Blantyre, babban birnin kasuwancin kasar.

An dai karkata akalar jirage dadama zuwa wasu wuraren, tun suna sama, kuma an umarci fasinja da dama dake jiran jirgi su je Lilongwe, babban birnin kasar mai nisan kilomita fiye da dari biyu.

Ministan sufuri na kasar, Ulemu Chilapondwa yace, an rufe filin saukar jiragen saman ne saboda an gono ramuka akan hanyar da jirgi yake sauka.