Nigeria: Za a soma babban taron Kasa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An yi ta cece kuce kan babban taron

Idan an jima a yau ne ake sa ran shugaban kasar Nigeria Dr Goodluck Jonathan, zai kaddamar da babban taron tattaunawa makomar kasar.

Wakilai 492 ne za su halarci taron, wanda kuma ake sa ran za su kwashe wata uku suna tabka muhawara a kan batutuwan da suka addabi al'ummar Nigeria.

Sai dai wasu 'yan Najeriyar na zargin cewa taron bata lokaci ne kawai, saboda babu wata matsalar kasar da ba a san maganinta ba.

Gwamnatin Nigeria ta kafe cewa taron yana da matukar mahimmanci ga makomar kasar.