Sanusi Lamido ya maida martani

Image caption An dakatar da Malam Sanusi ne bayan ya bayyana cewa ba a saka wasu kudaden mai a lalitar gwamnati ba.

Dakataccen gwamnan babban bankin Nigeria Malam Sanusi Lamido Sanusi ya musanta dukkanin zarge zargen da majalisar kula da kudade ta Nigeria ta yi masa a rahoton da ta baiwa shugaban kasa.

Malam Sanusi ya ce ya fara ganin rahoton da ake zargin sa da saba dokokin babban bankin kasar ne a lokacin da gwamnati ta mika masa takardar dakatarwa.

A cewar Sanusi Lamido da an nemi bayani tun farko, da an samu gamsasshiyar amsa a kan dukkanin abubuwan da ake da tantama a kan su cikin sauki.

Tsohon gwamnan bankin Najeriyar ya kuma yi kira ga shugaban kasar da ya sake duba dakatarwar da ya yi masa a matsayin gwamnan babban bankin kasar