Majalisar Crimea ta ayyana 'yancin kai

Mutane a yankin Crimea bayan bayyana sakamakon kuri'ar
Image caption Mutane a yankin Crimea bayan bayyana sakamakon kuri'ar

Majalisar dokokin Crimea a hukumance ta ayyana 'yancin kai daga Ukraine, inda suka nemi hade wa da Rasha.

Ta kuma sanar da mallake duk wasu gine-gine na Ukraine da ke yanki, kuma dokokin Ukraine sun daina amfani a Crimea.

Haka kuma majalisar ta nemi Majalisar Dinkin Duniya da kasashen duniya, su amince da 'yancin yankin.

Tun da fari jama'a a Simferopol, babban birnin Crimea sun yi ta shagulgula, saboda sakamakon farko na kuri'ar raba gardama na nuna cewa kashi 95 cikin dari sun zabia sake hade wa da Rasha.

Takunkumi

To sai dai bayan kammala zaben, Fadar white house ta fitar da wata sanarwa inda ta sake nanata cewa, Amurka ta yi watsi da zaben kuma ba zata amince da sakamakon zaben ba.

Sanarwar ta ce an gudanar da zaben ne karkashin yanayi na barazana da kuma tsoratar wa daga sojin Rasha.

Shugaba Obama ya ce a shirye Amurka da Tarayyar Turai su ke su kara kakaba takunkumi akan Rasha, sakamakon matakin da ta dauka a Ukraine.

Karin bayani