An rufe makarantun sakandare a Borno

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Bukatar Boko Haram ita ce addaina karantun Boko.

Gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima ya bada umurnin rufe makarantu sakandare 85 mallakar gwamnatin jihar saboda matsalolin tsaro.

Matakin gwamnatin nada nufin kare lafiyar dalibai da malamansu su 115,000 bisa fargabar fuskantar hare-hare daga wajen 'yan Boko Haram.

Umurnin gwamnatin ya shafi makarantun kwana da kuma na jeka ka dawo.

'Yan Boko Haram na kai hare-hare a kan makarantu inda suke kashe dalibai da dama tare bankawa gine-gine wuta.

A cikin makwannin da suka wuce ne Gwamnatin Tarayyar Nigeria ta bada umurnin rufe makarantun sakandare na tarayya guda biyar a jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa.

Hakan ya biyo bayan harin da 'yan Boko Haram suka kai a kan wasu dalibai a kwalejin gwamnatin tarayya dake Buni Yabi a jihar Yobe inda suka kona makarantar tare da kashe dalibai da dama.

Karin bayani