Crimea: EU ta saka wa 'yan Rasha takunkumi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Taron ministocin da aka yi a Brussels.

Ministocin harkokin wajen Tarayyar Turai da ke taro a birnin Brussels, sun amince su sa takunkumi a kan jami'an Rasha da na Ukraine su ashirin da daya, ta hanyar hana su yin tafiye-tafiye, da kuma taba kadarorinsu.

Ba a bayyana sunayen mutanen ba, to amma an ce sune ke da alhakin shirya kuri'ar raba-gardamar da aka kada a yankin Crimea, inda masu neman ballewa daga Ukraine domin hadewa da Rasha suka sami babban rinjaye.

Babbar jami'ar diplomasiyyar Turai Catherine Ashton ta ce, dole su yi tunani a tsanake kan irin martanin da za su mayar game da matakin hadewar Crimea da Rasha.

Tun farko dai, ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta yi kiran da a kafa wani kwamitin da zai taimaka wajen warware matsalar ta fuskar diplomasiyya.

Majalisar dokokin Crimea ta fito fili ta bayyana samun 'yancin kai daga Ukraine, kuma ta mika takardun neman hadewa da Rasha.

Majalisar ta ce, a yanzu dokokin Ukraine basu da tasiri a Crimea, kuma dukan kadarorin gwamnatin Ukraine da ke yankin, zasu zama mallakin Crimea.

Karin bayani