An kafa kwamitin sulhu da Boko Haram

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan Boko Haram

Shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan ya kafa kwamitin da zai tattauna da 'yan Boko Haram a kokarin kawo kashen zubar da jini a arewacin kasar.

Kwamitin mai wakilai bakwai zai yi kokarin sulhu da 'yan Boko Haram don su ajiye makamansu, su kuma karbi afuwa tare da tsagaita wuta.

Ministan ayyukan na musamman, Alhaji Kabiru Tanimu Turaki wanda zai shugabanci kwamitin, ya tabbatarwa BBC cewar kwamitin zai yi aiki ne a cikin sirri.

A baya gwamnati ta yi kokarin tattaunawa da 'yan Kungiyar Boko Haram amma kuma sai shugaban kungiyar Abubakar Shekau ya ce ba za su yi sulhu da gwamnati ba.

'Yan Boko Haram sun kaddamar da hare-hare a musamman jihohin arewa maso gabashin kasar inda suka hallaka mutane dubbai tare da kona gine-gine.

Karin bayani