An sake tsarin aikin neman jirgin Malaysia

Aikin neman jiirgin saman Malaysia Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Aikin neman jiirgin saman Malaysia

Amurka ta ce tana shirin janye daya daga cikin jiragen sojinta na ruwa daga aikin neman jirgin saman Malaysian nan da ya bace.

Amurkan ta ce za ta yi hakan ne domin sake tsarin aikin.

Ta ce jiragen saman bincike guda biyu da take da su a yankin, za su fi bincika wurare masu yawa fiye da jirgin ruwan.

Amurkan ta ce, jirgin ruwan me suna U-S-S Kidd ya gudanar da bincike a wani yanki a cikin kwanaki goma, a wurin da jirgin sama zai iya a tashi daya cikin sa'oi tara.

Yanzu dai sama da kasashe 25 ne ke aikin neman gano jirgin saman na Malaysia da ya bace da mutane 239, tun ranar takwas ga watan Maris akan hanyarsa daga Kuala Lumfur zuwa Beijin.

Ministan sufurin Malaysia , Hishamuddin Hussein ya ce, jami'an kasarsa ba sa boye komai dangane da lamarin tun da ya auku.