Fulani sun dakatar da tattaunawa da Berom

Al'ummar Fulani a Jihar Filato dake tsakiyar Nigeria ta dakatar da duk wata tattaunawa tsakaninta da al'ummar Berom a kokarin sulhunta rikici a jihar.

Kungiyar Fulani ta bayyana matsayinta ne a wata wasika da ta aike wa wata kungiyar mai zaman kanta mai suna Centre for Humanitarian Dialogue- CHD wacce ke kokarin sasanta tsakanin Fulani da Berom.

Kungiyar Fulani ta ce ta dauki matakinne saboda abinda ta ce yawaitar satar shanu da ake yi cikin makwanni biyun da suka wuce.

Al'ummar Fulani ta kuma koka game da abinda ta ce kashe mata mutane biyu tare da sace shanu 40 a farkon wannan watan.

Kawo yanzu kungiyar al'ummar Berom ba ta maida martani ba.

Fulani da Berom sun shafe shekaru suna rikici a tsakaninsu abinda ya janyo rasuwar mutane da dama tare da jikkata daruruwa da kuma hasarar dukiya mai dinbim yawa.

Karin bayani