Miyetti Allah za ta kawo karshen rikici

Image caption Wasu sassa na Najeriya sun dade suna fama da rikicin Fulani makiyaya da manoma

Kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah, Kautal Hore ta lashi takobin kawo karshen rikicin fulani makiyaya da manoma da wasu al'ummomi a Najeriya cikin watanni biyu.

Kungiyar wadda ta yi wannan ikirari bayan wani taro da ta yi da shuwagabannin Fulani daga jihohi daban daban a Nassarawan Eggon da ke jihar Nassarawa, ta ce, wadanda ke da alhakin magance rikicin ba sa yin abin da ya kamata, don magance lamarin.

Kungiyar ta yi zargin cewa gwamnonin jihohin da abin ya shafa, ba sa amfani da jagororin da ya kamata su yi amfani da su wajen shiga tsakani.

Shugaban kungiyar ta Miyetti Allah Kautal hore na Najeriya Alh. Bello Abdullahi Bodejo shi ya furta kalaman.