Majalisar Nigeria na binciken mutuwar matasa

Minsitan cikin gida na Najeriya, Abba Moro Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Minsitan ya ce bincike ya kamata a yi, ba batun murabus ba

Majalisar dattawan Najeriya ta umarci kwamitinta da ke kula da harkokin cikin gida, ya yi bincike a kan mutuwar matasan da ya auku a ranar Asabar.

Kimanin matasa 20 ne suka mutu a wani turmutsitsin shiga guraren da ake jarrabawar daukar ma'aikata, a hukumar shige da fice a wasu sassan kasar.

Wasu daga cikin 'yan majalisar sun bukaci a dakatar da ministan harkokin cikin gida Patrick Abba Moro, bisa zargin sakacinsa ne ya janyo al'amarin.

Yayin da wasu kuma suka bukaci gwamnatin tarayya ta gaggauta kafa wata gidauniya da za ta mayar da hankali wajen sama wa matasa aikin yi.