Ba 'yan siyasa bane maganin rikicin Fulani

Kungiyar tuntubar juna ta musulmi da kirista ta jihar Kaduna sun ce yan siyasa ba za su iya magance rikicin makiyaya fulani da manoma ba.

Kungiyar ta ce ya kamata gwamnatoccin da wanan lamarin ya shafa su nemi sarakunan gargajiya da kuma ardodi akan yadda za'a shawo matsalar.

Kungiyar ta yi wanan kiran ne a dai dai lokacin da jama'a ke ci gaba da nuna alhinin kisan gillar da ka yi wa tarin jama'a a karamar hukumar Kaura da ke kudancin kaduna da kuma karamar hukunar Faskari da Sabuwa a jihar Katsina.

Kungiyar na gani akwai wasu abubuwa da dama da ya kamata a ce an yi domin samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a wadanan yankuna