Boko Haram: Gwamnoni na taro a Amurka

Image caption 'Yan Boko Haram sun kashe mutane da dama a Nigeria

Wasu gwamnonin Arewacin Nigeria suna wata tattaunawa a Amurka a kokarin lalubo hanyoyin kawo karshen ayyukan 'yan Boko Haram.

Gwamnonin sun tattauna da jami'an gwamnatin Amurka a cibiyar samar da zaman lafiya dake Washington, inda rahotanni suka ce sun shafe sa'o'i da dama suna musayar ra'ayoyi game da batun.

Gwamnatin Amurka tare da hadin gwiwar gwamnatocin Norway da Denmark ne suka dauki nauyin tattaunawar.

Baya ga batun tsaro, bayanai sun nuna cewar za a tattauna kan hanyoyin bunkasa tattalin arzikin yankin da kuma yadda za a samar da ilimi ga yara.

Daga cikin gwamnonin da suka halarci taron, akwai Kashim Shetttima na Borno da Isa Yuguda na Bauchi da Babangida Aliyu na Niger da Murtala Nyako da Adamawa da kuma Aliyu Magatardar Wamakko na jihar Sokoto.

Sauran sune Rabiu Kwankwaso na Kano da Ibrahim Shema na Katsina da Saidu Dakingari na Kebbi da Ibrahim Dankwambo na Gombe da Abdulfatah Ahmed na Kwara da kuma gwamnan Zamfara Abdulaziz Yari.

Karin bayani