Ukraine na shirin janye dakarunta daga Crimea

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dakarun Rasha sun kewaye sansanin.

Babban jami'in tsaro a Ukraine, Andriy Parubiy, ya ce gwamnatinsa ta soma shirye-shiryen janye dakarunta da iyalansu daga Crimea, bayan da Rasha ta mamaye tsibirin.

Ya ce, shirin zai basu damar komawa kasar Ukraine cikin gaggawa, ba tare da wani cikas ba.

Duk da cewa shiri ne na ko-ta-kwana, in ji masu aiko da rahotanni, wannan ne karon farko da wani mamba na sabuwar gwamnatin Ukraine, ya fito fili yayi magana a kan janyewa daga Crimea.

Jami'an tsaron ya kuma ce, Ukraine na shirin yin atisayen soja tare da Amirka da kuma Birtaniya.

Tun farko dai daruruwan magoya bayan Rasha da ke dauke da makamai sun dira a kan wani sansanin sojin ruwan Ukraine da ke birnin Sevastopol na yankin Crimea.

Hakan ya auku ne kwana daya bayan amincewar da Rasha ta yi ta sanya yankin na Kirimiya a cikin kasarta.

Ukraine ta ce an yi awon gaba da kwamandan sojin ruwanta daga sansanin.

Kawo yanzu dai an kafa totocin Rasha a cikin ginin.

Haka kuma dakarun Rasha sun kai hari a wani sansanin sojin ruwan Ukraine dake Novoozerne a yammacin Crimea.

Gwamnatin Ukraine din ta ce an hana ministocinta biyu shiga cikin yankin Crimea.

Karin bayani