'Mutane 5 sun mutu a harin Soji a Borno'

Image caption Dakarun Nigeria na farautar 'yan Boko Haram

Rahotanni daga kauyen Kayamla da ke karamar hukumar Konduga a jihar Borno na cewa sojoji sun kai hari da jirgin sama, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla biyar, ya yin da wasu kuma suka jikkata.

Hakan ya biyo bayan wata wasika da mazauna garin suka ce wasu 'yan bindiga sun kai bariki dake cewa za su kara kai hari.

Wasu rahotannin sun ce 'yan Boko Haram da aka kubutar daga Barikin Giwa sun samu fake wa a kauyen, abin da ya sa sojojin suka kai farmaki da jirgin sama a kauyen.

A ranar Juma'ar da ta gabata ne aka kai hari barikin sojoji na Giwa, abin da ya janyo mutuwar sama da mutane 100, ciki har da fararen hula, bayan soji sun kai farmaki a kan maharan.

Karin bayani