Za a mika Ble Goude ga kotun ICC

Charles Ble Goude
Image caption Charles Ble Goude tare da dakarun sa kai

Kasar Ivory Coast ta amince ta mika wani tsohon shugaban matasa sojin sa kai da ya yi kaurin suna, Charles Ble Goude, ga kotun manyan laifuka ta duniya dake a Hague.

Kotun dai na nemansa ne ruwa a jallo a kan tuhumar aikata liafukan cin zarafin bil adama, kuma a halin yanzu ana tsare da shi ne a gidan yari.

A cikin watan Oktoba, kotun ta duniya ta bayar da sammacin kama Mr Ble Goude, wanda ya jagoranci matasa sojin sa kai masu kishin kasa da suka fafata a kan tituna zamanin shugabancin Laurent Gbagbo.

Karin bayani