An kashe mahara 4 a Afghanistan

Sojojin Afghanistan Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sojojin Afghanistan

Jamian tsaro a Afghanistan sun ce sun karbe iko a wani otel dake Kabul babban birnin kasar bayan sun kashe matasa hudu da suka kaiwa wurin hari.

Kakakin gwamnati ya ce maharan masu shekaru kasa da 18 sun shiga cikin otel din da kananan bindigogi da suka boye a cikin safasu, inda suka ce suna son su ci abinci.

Sai dai ya ce ya yinda suka yi kokarin aiwatar da harin, ba 'a ba ta lokaci ba wajen mayar masu da martani

Kakakin ya ce babu wani bako da ya sauka otel din da ya ji rauni sai dai mutane akala biyu sun jikkata.

Kungiyar Taliban ta yi ikirarin cewa ita ce ta kai harin.