Mata 9 sun haihu a sansanin Katsina

Dan Fulani na jin radiyo a yayin da yake kiwon shanu
Image caption Matan na zuwa gidajen mazauna garin da sansanin yake, domin su yi wankan jego

Hukumomi a jihar Katsina dake arewacin Nigeria sun ce, mata tara ne suka haihu a sansanin da aka tsugunar da masu neman mafaka.

Daruruwan jama'a na zaune a sansanin ne, sakamakon hare-haren da wasu 'yan bindiga suka kai, wasu yankuna na jihar, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da 100.

Hukumomin sun ce har yanzu mutanen sun kasa komawa gidajensu, saboda fargabar sake kai musu hare-hare.

Tuni dai masu lura da al'amura suka fara jan kunne kan matsalar tsaro da za a iya fuskanta, idan har ba a tunkari kalubalen dake tattare da irin wadannan hare-hare ba.