Malaysia: Australia na duba tarkace

Image caption Abubuwan da ake zaton tarkacen jirgin ne

Kasar Australia na duba wasu abubuwa biyu da tauraron dan adam ya hango, wadanda ake zaton tarkacen jirgin Malysia ne a tekun India.

Jirgin ruwa na kasar Norway da shiga binciken da jiragen sama na Australia da Amurka da New Zealand the ke yi kilomita 2,500 daga Perth.

Ya ce hukumar kiyaye haddura ta ruwa ta Australia ita ce ta sami bayani kan wasu hotunan tauraron dan-adam na wasu abubuwa da ka iya kasancewa masu alaka da jirgin.

Australian ce dai ke jagorantar aikin binciken da ake na jirgin saman na Malaysia da ya bace kusan sati biyu, daga bangaren kudu, da ya kama daga yammacin Australia ya zuwa gabar tekun Indonesia.