Amurka zata bunkasa arewacin Nigeria

Gwamna Mu'azu Babangida Aliyu Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Gwamnonin na cike da kyakkyawar fata game da taron

Gwamnonin jihohin arewacin Najeriya, sun tattauna da wasu manyan jami'an gwamnatin Amurka da 'yan kasuwa game da yankin.

Taron wanda Amurka ta dauki nauyi na duba yadda za a taimaka wajen habaka tattalin arzikin yankin da kuma magance matsalar tsaro.

Yankin arewacin Najeriyar na fama da talauci da karancin ilimi da kuma tabarbarewar tsaro.

Gwamnoni yankin 13 ne dai suka halarci taron wanda ake yi a birnin Washington.