'APC na barazana ga gwamnatin Jonathan'

Jam'iyyun APC da PDP Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jam'iyyun APC da PDP

Jam'iyyar PDP me mulki a Najeriya ta zargi jam'iyyar adawa ta APC da shirya wata makarkashiya ta hambarar da gwamnatin PDP.

A cikin wata sanarwa da Sakataren Yada labaran PDPn na kasa, Chief Olisa Metu ya fitar a jiya, jam'iyyar ta sake nanata zargin da taba yi cewa, jam'iyyar APC na shirin wargaza gwamnati Jonathan.

Ta kuma ce a jam'iyyar APC na son ta raba Najeriya, ta hanyar amfani da masu tayar da kayar baya wajen hambarar da gwamnatin PDP.

Sai dai a nata bangaren, jam'iyyar adawa ta APCn a martaninta game da zargin kifar da mulkin dumukradiyyar a Najeriya da PDP ta yi mata, ta ce kalaman da PDPn ta yi ba su bata mamaki ba tana mai cewa ruwa ne ya ciyota, kuma shure-shure ba ya hana mutuwa.